Staffan de Mistura zai ajiye aikinsa kan Siriya
October 17, 2018Talla
Jami'in diflomasiyar wanda shekarunsa 71 a duniya zai ajiye mukamin ne a wata mai zuwa kamar yadda ya fada wa kwamitin sulhun Majaliar Dinkin Duniya a birnin New York.
De Mistura ya ce wannan ajiye mukamin nasa ya yi shi ne don wasu dalilai da suka shafe shi. Ya dai ba da muhimmiyar gudunmawa a kokarin ganin bangarorin da ke fada da juna a rikicin na Siriya da ya faro a shekarar 2011 sun koma kan teburi don warware matsalar da har kawo yanzu ta gagara.
De Mistura ya ce zai yi amfani da makon da ya saura a wannan aiki wajen ganin an samar da kwamitin da zai yi aiki wajen ganin an samar da sabon kundin tsarin mulki ga kasar Siriya.