1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jakadan Siriya ya yi sauyin sheƙa

Zainab MohammedJuly 12, 2012

Nawaf Fares jakadan Siriya a Iraki ya ajiye mukaminsa tare da sanar da haɗewa da 'yan tawaye, a wani mataki na nuna adawa da halin da ake ciki a ƙasarsa.

epa03282895 A handout picture released by the official Syrian Arab News Agency SANA on 26 June 2012 show Syrian president Bashar al-Assad speaking during his meeting with the new Syrian government in Damascus, Syria, 26 June 2012. EPA/SYRIAN NEWS AGENCY SANA / HANDOUT HANDOUT EDITORIAL USE ONLY/NO SALES +++(c) dpa - Bildfunk+++
Hoto: picture alliance/dpa

Jakadan Syria a Iraki, Nawaf Fares yayi sauyin sheƙa zuwa ɓangaren 'yan adawa, tare da kira ga sojojin ƙasar da su juya bakin bingigarsu zuwa kan gwamnati. Wannan dai shine babban jami'in gwamnatin Bashar al-Assad na farko, da ya juya wa gwamnatin na siriya baya. A sakon da kafafen yaɗa labarai suka gabatar, Fares yace ya janye daga jam'iyyar da ke mulki ta Baath tare da barin mukaminsa a matsayin jakadan gwamnati. Kazalika ya yi amfani da wannan dama wajen kira ga sauran 'yan jam'iyyar Baath dake mulki, da su yi watsi da gwamnatin Bashar al-Assad.

Majiyar diplomasiyya ta shaidar da cewar, tuni jami'in diplomasiyyan na Siriya ya mika wasikarsa ta barin aiki wa magabatan Iraki, kuma wani lokaci a yau ne zai gana da magabatan na Iraki.

Mawallafiya: Zainab Mohammed Abubakar

Edita           : Umar Saleh Umar