1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jama'a na kaɗa ƙuri'a a zaɓen Iran

June 14, 2013

Mutane kusan miliyan 50 ake sa ran za su fito a zaɓen na shugaban ƙasa da ke gudana cikin tsauraran matakai tsaro.

Iran's Supreme Leader Ayatollah Ali Khamenei casts his ballot at his office during the Iranian presidential election in central Tehran June 14, 2013. Iranians voted for a new president on Friday urged by Khamenei to turn out in force to discredit suggestions by arch foe the United States that the election would be unfair. REUTERS/Fars News/Hassan Mousavi (IRAN - Tags: POLITICS ELECTIONS TPX IMAGES OF THE DAY) ATTENTION EDITORS - THIS IMAGE WAS PROVIDED BY A THIRD PARTY. FOR EDITORIAL USE ONLY. NOT FOR SALE FOR MARKETING OR ADVERTISING CAMPAIGNS. THIS PICTURE IS DISTRIBUTED EXACTLY AS RECEIVED BY REUTERS, AS A SERVICE TO CLIENTS
shugaban addinin Iran, Ajatollah Ali Khamenei ke kada ƙuri'arsaHoto: REUTERS/Fars News

Yanzu haka An buɗe rumfunan zaɓe a ƙasar Iran, inda jama'a suka fara kaɗa ƙuri'a domin zaɓen mutumin da zai gaji Mahmud Ahmadinejad a matsayin shugaban ƙasa wanda shi ba zai tsaya takara ba, bisa dokar ƙasar.

Mutane kimanin miliyan 50 ake sa ran za su kaɗa ƙuri'unsu a zaɓen da 'yan takara shida za su kara. A ciki har da Said Jalili babban mai sasantawa na ƙasar ta Iran tsakaninta da ƙasashen yammancin duniya, a kan shirinta na nukiliya wanda kuma ke ɗaya daga cikin 'yan takarar waɗanda ake zaton za su taka rawar gani a zaɓen.

Baya ga zaɓen shugaban ƙasa dai Iraniyawan har da na 'yan majalisar dokoki da na ƙananan hukumomi za su zaɓa a yau ɗin.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane

Edita : Usman Shehu Usman