1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Fada ya kara muni a Nagorno Karabakh

Abdourahamane Hassane
September 26, 2023

Dubban mazauna Nagorno Karabakh na tserewa daga yankinsu zuwa Armeniya inda akalla mutum dubu 13,000 daga cikinsu suka samu mafaka.

Hoto: Alexander Patrin/TASS/dpa/picture alliance

Mako guda bayan farmakin da Azarbaijan ta kai a wannan yanki nata na Caucasia mai neman ballewa wanda aksarin mutanen yankin na magana ne da harshen armeniya.A yau kungiyar Tarayyar Turai a birin brussel za ta tattauna da wakilan Armeniya da na  Azerbaijan, tsoffin manbobi a jamhuriyar Tarayyar Soviet da suke ta yin artabu a kan yankin na Nagorno domin samar da zaman lafiya.