1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jama'ar Laberiya sun kada kuri'a a zaben shugaban kasa

Usman Shehu Usman ATB
December 26, 2017

Al'ummar Laberiya sun yi fitowar dango inda suka kada kuri'a a zaben shugaban kasa tsakanin George Weah da mataimakin shugaban kasa Joseph Boakai domin zabar wanda zai gaji shugaba Ellen Johnson Sirleaf

Liberia Wahlen 2017
Hoto: Reuters/T. Gouegnon

Su dai wadannan mutane biyu da ke fafatawa duk sun yi fice a idanun 'yan Laberiya, inda Joseph Boakai ya kasance mataimakin shugaban kasa tun shekarar 2006, kuma yake da matukar karbuwa wajen 'yan boko da 'yan kasuwa, yayin da shi kuma George Weah fuskarsa ta kasance ba bakuwa ba a cikin Laberiya da sauran kasashe na duniya kasancewarsa zakaran kwallon kafa na duniya musamman kyautar gwanin kwallon kafa na duniya da ya taba samu.

Kasancewar George Weah matashi kuma wanda ya yi matukar daga sunan Laberiya a duniya bisa kwarewarsa wajen kwallon kafa, hakan ya bashi matukar farin jini musamman a tsakanin matasan Laberiya, inda ma a zaben da ya gabata da kyar shugaba mai ci Ellen Johnson Sirleaf ta kada shi.

Bukatar zaman lafiya a Liberiya

Tsohon zakaran kwallon kafa George WeahHoto: AFP/Getty Images/Z. Dosso

Bayan kada kuri'arsa a wannan Talata, George Weah ya fada wa manema labarai sakonsa ga 'yan Laberiya.
"Sakon zaman lafiya da dorewar kasarmu. Yau ne 'yan Laberiya ke nuna zabinsu, za su zabi shugaba.  Ba abin da ya hada ni da faduwar zabe. Yau nasara za ta tabbata,  Boakai ba zai kada George Weah ba.  Ellen Johnson ta kada ni saboda dalilai na daban, amma abin da ya faru a baya ba zai sake faruwa ba."

Shi kuwa a jawabinsa mataimakin shugaban kasa da ke neman shugabancin kasar, Joseph Boakai a wani taro na musamman da ya yi da al'ummar Fulanin kasar Laberiya ya shaida wa Fulanin bukatar da yake da ita ga kasar Laberiya, musamman kan makomar kasar bayan zabe. 

Hadin kan 'yan Laberya
"Dukkanmu da ni da George Weah yayin da muke jiran sakamkon zabe, ya kamata ko wannenmu ya rungumi kaddara ya amince da shan kaye idan ya fadi. Don mu kawo zaman lafiya a kasarmu. Mu yi tunani ga makomar jama'armu bisa ukubar da suka gani a baya."

Mataimakin shugaban kasa Joseph BoakaiHoto: Reuters/T. Gouegnon

Hukumar zaben Laberiya dai za samu kanta cikin tsaka mai wuya bayan gudanar da zagayen farko na zaben, inda mataimakin shugaban kasa da magoya bayansa suka yi zargin aringizon kuri'u abin da ya kai ga kotun kasar ta dage lokacin gudanar da zaben zagaye na byiu. Sai dai a wannan karon shugaban hukumar zaben Jerome Korkoya, ya ce ya zama wajibi hukumar ta yi zabe mai tsabta.

Zabe mai tsabta
"Hakika ba mu da zabi. Alhakinmu ne mu gudanar da zabe mai gaskiya da adalci mu yi zaben da 'yan Laberiya su kansu za su amince da shi."

Za dai a iya cewa zaben ya gudana cikin kwanciyar hankali, domin babu rahotannin wani tashin hankali  da aka samu. Wannan zaben dai zai kasance zakaran gwajin dafi ga dorewar demokradiyya a kasar Laberiya wacce tarihi ba zai manta da mummunan yakin basasa da kasar ta fada ciki a shekarun baya ba.