1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Faransa ta mayarwa Benin kayan tarihinta

November 11, 2021

Al'ummar Jamhuriyar Benin na ci gaba da gudanar da bukukuwa, domin nuna murna da mayar da kayan tarihi kimanin 26 da sojojin mulkin mallaka na Faransa suka sace daga kasar.

Benin | Rückkehr von Kunstobjekten in Cotonou
Shugaba Patrice Talon na Jamhuriyar Benin Hoto: Séraphin Zounyekpe

A ranar Laraba ne dai kayan tarihin suka isa babban birnin kasar Cotonou, inda daga bisani aka garzaya da su fadar shugaban kasar wanda suka sami rakiyar tawagar mutane a kan dawakai. Mayar da kayan tarihin dai na zuwa ne, bayan kiraye-kirayen da Afirka ke yi wa kasashen yamma da su dawo da ganimar da suka kwasa daga gidajen tarihi a zamanin mulkin mallaka.

Karin Bayani: Birtaniya za ta mayar da kayan tarihin Benin

A ranar Litinin din da ta gabata ce dai shugaban kasar Patrice Talon da ministan al'adu suka yi tattaki zuwa birnin Paris na Faransa domin karbo kayan tarihin na kasarsa, a wani mataki na cika alkawarin da gwamnatin Faransan ta dauka na mayarwa Benin din da Senegal da ta mulka kayan tarihinsu da sojojinta suka sace a lokacin mulkin mallaka. A jawabinsa ga al'ummar kasar, Shugaba Talon na Benin ya ce: "Ba zan daina nuna godiyata da karamcin da Benin ta ba ni na dan wani lokaci ba, na gode da amanar da kuka ba ni da kuma alfaharin da kuka yi da ni wanda ke bayyana cikin nasarorin da muke samu a kullum."
Daga cikin kayayyakin da aka dawo da su har da kujerar sarautar Sarki Ghezo da ya mulki masarautar Abomey da ke kudancin Benin a shekarun 1818 zuwa 1858, abin da ya faranta zukatan sarakai dabam-dabam na kasar. A cewarsu, hakan zai kara bai wa matasan kasar damar sanin tarihi da kuma al'adun da aka gada tun zamanin kakkanni. A nasa jawabin Mai martaba sarkin Kika Gnangorosuambou cewa ya yi: "Muna mika godiya ga shugaban kasa tare da shugaban kasar Faransa. Shugabannin biyu sun hada gwiwa don tabbatar da mafarkinmu ya zama gaskiya. A tunanina akwai bukatar matasa su sanya sha'awar zuwa gidan tarihin da za a gina wa kayayyakin tarihin, saboda matasan ba su da masaniya a fannin al'adu."

Kayan tarihin Jamhuriyar Benin sun koma gida daga FaransaHoto: Séraphin Zounyekpe

Karin Bayani: Jamus na shirin mayar da kayan tarihin Benin

Al'ummar kasar da dama dai sun baro garuruwansu don halartar bikin karbar kayayyakin tarihin da suke jin labaransu. Tuni dai sauran kasashen Afirka suka bukaci kasashen Birtaniya da Beljiyam da Holland da kuma Jamus, su mayar musu kayan tarihin da suka sace lokacin mulkin mallaka. A watan da ya gabata ma dai, Najeriya ta ce ta cimma yarjejeniya da Jamus kan mayar mata da kayan tarihin da aka sace a karni na 16 zuwa 18 a fadar tsohuwar masarautar Benin.

 

 

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani