Gidan rawa ya rufta a Jamhuriyar Dominican
April 9, 2025
Shugaban kasar Jamhuriyar Dominican Luis Abinader ya ayyana kwanaki uku na zaman makoki a fadin kasar sakamakon ruftawar rufin wani gidan rawa a farkon makon nan, wanda ya rista da rayukan mutane kusan 100. Wannan na zuwa a daidai lokacin da darruruwan masu aikin ceto ke ci gaba da aiki domin lalubo mutane da ake kyauta zaton suna da sauran numfashi.
Sabbin alkaluma da hukumomin Jamhuriyar Dominican suka fitar a wannan Laraba na nunar da cewa adadin mutanen da suka mutu a sakamakon ruftawar rufin gidan rawar ya karu zuwa mutum 98, yayin da adadin wandanda suka jikkata ya tashi a mutum 150.
Wannan mummunan ibtila'i ya auku ne a daren Litinin wayewar Talata a lokacin da fitaccen mawakin kasar Rubby Perez ke tsaka da gwangwaje wa a gaban 'yan kallo kusan 1,000 da suka zo dafifi domin rayawa a kataferen wasan da ya shirya a gidan raye-raye da ake wa lakabi da Jet Set da ke Sainto-Domingo babban birnin kasar.
Yayin da jami'an ceto sama da 400 ke ci gaba da aiki domin zakulo mutanen da ke da sauran nufashi, darurrruwan mutane sun yi wa gurin da ibtila'in ya auku kawanya, a gefe guda wasu kuma na kai kamo zuwa asibitoci domin samun labarin 'yan uwa da danginsu.
Wannan ibtila'i da ke zama mafi muni da Jamhuriyar Dominican ta fuskanta a 'yan shekarun nan bayan gobarar da ta tashi a wani gidan yari a 2005 wadda ta halaka fursunoni 136, ya kuma ritsa da rayukan fitattun mutane da dama ciki har da gwamnar lardin Monte Cristi da ke arewa maso gabashin kasar da kuma wasu tsoffin fitattun 'yan wasan kwallon kwando baya ga shi kan sa fitacce mawakin Rubby Perez wanda har kawo wannan lokaci dabu tabbas a game da mokamarsa.
A wannan safiya shugaban kasar Luis Abinader ya ziyarci gurin da lamarin ya auku tare da ayyana kwanaki uku na zaman makoki a fadin kasar domin girmamawa ga wadanda wannan ibtila'i ya ritsa da rayukansu.