An kashe sojojin Jamhuriyar Nijar
May 3, 2021A cewar sanarwar da sakataren tsaron yankin Ibrahim Miko ya yi wa gidan talabijin da maraicen jiya.
Daga cikin wadanda ajalin nasu ya sauka harda laftanar Mamman Manewa da ke zama kwamandan rundunar. Ire-iren wadannan hare-haren dai an jima ana aiwatar da su, ko a watan Maris din da ya gabata a wannan yankin da ke makwabtaka da Kasar Mali da Burkina Faso an kai wa wasu kauyuka uku hari da kuma ya yi sanadiyar rayuka sama da mutum 140. harin da ke zama mafi muni da ya auku a kasar.
Tun a shekarar 2012 ayyukan ta'addanci ke aukuwa a wannan yankin da ma kasashen da ke makwabtaka da shi.
A baya dai kungiyoyin da ke mubaya'a da Al-Qaeda da kuma IS sun sha daukar alhakin hare-haren da ya gudana, sai dai ya zuwa yanzu babu wata kugiya da ta dauki alhakin wannan da ke zama na baya-baya.