1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Jamhuriyar Nijar: Sabuwar dokar hukunta alkalai

Gazali Abdou Tasawa SB
August 22, 2025

Mahawara ta kabre a Jamhuriyar Nijar kan batun dacewar wata sabuwar dokar musamman da gwamnatin mulkin sojan kasar ta kira da cewa dokar da'ar aikin alkalai ta zamanin sabuwar tafiyar kasar.

Shugaban gwamnatin mulkin sojan Nijar Janar Abdourahmane Tiani
Shugaban gwamnatin mulkin sojan Nijar Janar Abdourahmane TianiHoto: Gazali Abdou/DW

A Jamhuriyar Nijar, mahawara ce ta kabre a kasar a kan batun dacewar wata sabuwar dokar musamman da shugaban gwamnatin mulkin sojan kasar Janar Abdourahmane Tiani ya sa wa hannu da ya kira dokar da'ar aikin alkalai ta zamanin sabuwar tafiyar kasar Nijar a karkashin mulkin soja da aka fi sani da "refondation”. Wanann sabuwar doka ta bai wa shugaban kasar damar jingine dokar hukunta alkalai ta kasa da ke da akwai, domin yin gaban kansa wajen dokar matakin hukunta alkalai da za a samu da aikata wasu manyan laifuka a kasa.

Karin Bayani: Muhawara kan yawan albashin majalisar rikon kwarya a Nijar

Dokar wacce shugaba Tchiani ya sa wa hannu a ranar 14 ga wannan wata na Agustan 2025, ta bai wa shugaban kasar hurumin daukar duk wani mataki da yake ganin ya dace domin hukunta duk wani alkali da za a samu da aikata wani babban laifi ko kuma samun shi da hannu dumu-dumu a cikin wata barna, ko kuma nuna wata dabi'a ta neman cin zarafin wata hukumar jamhuriya. Kuma dokar wacce shugaban kasar ya kira ta da'ar aikin alkalai, doka ce mai ribas da ka shugaban kasa ka iya amfani da ita wajen hukunta alkalan da suka aikata wasu manyan laifuka kafin samar da dokar da kuma laifukan da za su iya aikatawa a nan gaba.

Shugaban gwamnatin mulkin sojan Nijar Janar Abdourahmane TianiHoto: Boureima Hama/AFP

Shugaban kasar ta Nijar ya dauki wannan dokar loakcin da ake ciki wani takun saka tsakanin ma'aikatar shari'a ta kasa da alkalai, takun sakar da ya kai ga rusa wasu kungiyoyin alkalan Nijar da ma soke sunayen wasu alkalan daga jerin alkalai na kasa. Kuma Dokta Mayra Djibrine wata ‘yar fafutika da ke da zama a Faransa bayyana sabuwar dokar ta yi da wani sale-sale na neman shinfida mulkin kama karya.

To sai dai wasu ‘yan Nijar din na cewa idan an bi ta barawa ya kamata a bi ta mabi sau domin kuwa ba shakka akwai bukatar gyara ga yadda alkalai ke tafiyar da harkokin shari'a a kasar. Kawo yanzu dai babu day adaga cikin kungiyoyin alkalan rusassu ko masu ran da suka yi tsokaci a kan wannan sabuwar doka wace ta zo a daidai loakcin da aka kafa wani kwamiti da zai nazarin hanyoyin sulhunta bangaren gwamnati da kungiyoyin alkalai, musamman wadanda gwamnatin ta rusa da ma soke wasu mambobinsu kwata-kwata daga jerin sunayen alkalan Nijar.

 

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani