1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Nijar ta soke dokar hukunta laifin safarar mutane zuwa Turai

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
November 28, 2023

Yankin Agadez na Jamhuriyar Nijar na zama wata babbar kofar ficewa zuwa Turai ta hanyar shiga Libya

Hoto: ORTN/Télé Sahel/AFP/Getty Images

Gwamnatin mulkin sojin Jamhuriyar Nijar ta soke dokar hukunta wadanda ake kamawa da laifin safarar mutane suna ketarawa Turai da su ta hamadar Sahara, wadda aka kafa shekarar 2015.

Wannan na cikin wata sanarwa da ma'aikatar shari'ar kasar ta fitar, mai dauke da sa hannun babban sakatarenta Ibrahim Jean Etienne, bayan amincewar shugaban mulkin sojin kasar Janar Abdourahmane Tchiani, kuma wadanda suke daure yanzu haka a kan laifin to za a sake su.

Karin bayani:Shugaban Nijar na ziyarar aiki a Mali da Burkina Faso

Wannan matakin na gwamnatin sojin Nijar din ka iya kara janyo takun saka tsakaninta da kasashen Turai da suka kakaba mata takunkumi, sakamakon hambarar da gwamnatin dimukuradiyya ta Mohamed Bazoum a cikin watan Yulin bana.

Karin bayani:Karar da Jamhuriyra Nijar ta shigar kotun ECOWAS

Yankin Agadez na Jamhuriyar Nijar na zama wata babbar kofar ficewa zuwa Turai ta hanyar shiga Libya, inda Majalisar Dinkin Duniya ta yi kiyasin cewa a duk mako daya akalla 'yan ci-rani dubu arba'in ne suke bi ta Agadez don shiga Turai ba bisa ka'ida ba.