1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamhuriyar Nijar ta yi sauye-sauye ga jarabawar dabilai

Gazali Abdou Tasawa SB)(ZMA
April 12, 2022

Gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta sake mayar da tsarin rijistar dalibai masu jarabawar Bakaloriya na shekarar bana ta hanyar Intanet abin da ya haifar da cece-kuce a cikin kasar da ke yammacin Afirka..

Oberschüler in Tahoua, Niger
Hoto: DW

A Jamhuriyar Nijar gwamnatin kasar ta sake maido da tsarin rijistar dalibai masu jarabawar Bakaloriya na shekarar bana ta hanyar Intanet. Sai dai a daidai lokacin da ya rage ‘yan kwanaki wa'adin yin kammala rijistar ya cika, kungiyar dalibai ta kasa ta USN ta nuna damuwarta kan wasu matsaloli da ta ce na tattare da shirin da suka hada da rashin intanet a yankunan karkara da kuma yadda wasu shugabannin makarantu ke karbar kudaden rijistar da suka zarce wadanda gwamnati ta tsaida.

Karin Bayani: Kokarin warware matsalar ilimi a Nijar

Wannan shi ne karo na biyu a tarihin kasar ta Nijar da gwamnati ke amfani da wannan kafa ta zamani ta Intanet wajen rijistar sunayen dalibai da ke son shiga jarabawar neman takardar Bakaloriya wacce ba wa dalibi damar shiga jami'a domin ci gaba da karatunsa. Malam Yahaya Sa'adou shi ne jami'in da ke kula da wannan tsari na rajistar daliban ta Intanet a ofishin kula da tsara jarabawar Bakaloriya a Nijar ya bayyana dalilan gwamnatin na fito da tsarin da suka hada da samun tsari na zamani, kuma daliban da babu intanet a garinsu suna iya zuwa babban gari mafi kusa.

Hoto: picture alliance / ZB

A shekarar da ta gabata dai an kai ruwa rana tsakanin dalibai da hukumar shirya jarabawar Bakaloriyar kafin daga karshe daliban su amince da shirin. Sai dai sun ce a bara an fuskanci kura-kurai wajen tafiyar da shirin. Kuma Boudou Issoufou mahamadou mataimakin babban magatakardan kungiyar daliban kasar Nijar ta USN ya ce duk da matakan da mahukunta suka dauka na gyara mafiyawancin matsalolin, har yanzu akwai saura da suke bukata a gyara.

Su kuwa kungiyoyin kare martabar ilimi a Nijar duk da yake ba sa adawa da tsarin na rijistar daliban masu jarabawar Bakaloriya ta Intanet, akwai bukatar gwamnati ta sa ido kan yadda wasu makarantun ke karbar a wajen daliban kudaden rijista wadanda suka zarce wadanda gwamnati ta tsaida. Alhaji Amadou Roufa'i Lawal shugaban kungiyar COAD na daga cikin masu irin wannan korafin.

Dalibai sama dubu 78 daga ciki ‘yan mata kusan dubu 30 ne dai suka rubuta jarabawar Bakaloriya a shekarar da ta gabata a fadin kasar ta Jamhuriyar Nijar. A bana yanzu haka ana ci gaba da rijistar sunayen daliban inda ya rage kasa da mako daya wa'adin da aka diba na yin wannan aiki ya cika. Kuma ana kyautata zaton adadin wadanda za su rubuta jarabawar bakaloriyar a bana a kasar ta Nijar, zai zarce na shekarar da ta gabata.