1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Komawa tafarkin dimukaradiyya a Jamhuriyar Nijar

January 26, 2024

Wannan ya biyo bayan jan kafa da ake ganin sojojin da suka kifar da gwamnatin Mohamed Bazoum a ranar 26 ga watan Yulin da ya gabata na yi wajen gabatar da jaddawalin dawo da kasar kan tafarkin dimokuradiyya.

Jamhuriyar Nijar | Yamai lokacin gangamin goyon bayan juyin mulki
Yamai lokacin gangamin goyon bayan juyin mulkiHoto: AFP/Getty Images

A kwana a tsahi watanni shida kenan da sojoji suka karbe madafun iko a Nijar bayan sun kifar da halastacciyar gwamnatin farar hula ta Mohamed Bazoum, wacce al'ummar kasar suka zaba. Sai dai bayan share wannan dogon lokaci cikin dambarwa da kiki-kika har kawo yanzu ba bu wasu alamu a game da wa'adin da sojojin suka dibar wa kansu domin dowo da mulki ga farar hula duk kuwa da matsin lamba daga kungiyar habaka tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika ECOWAS da ke da'awar a dawo da kasar kan tafarkin dimukudiyya cikin gajeren lokaci.

Karin Baynai: Matsalolin tsaro bayan juyin mulki a Nijar

Janar Mohamed Toumba lokacin gangamin goyon bayan juyin mulkiHoto: Balima Boureima/AA/picture alliance

A cikin wannan yanayi ne wasu shugabanni al'umma ciki har da sarakanunan gargajiya suka yi kira ga majalisar sojojin karkashin birgediya janar Abdourahaman Tiani da ta dauki iya lokacin da take ganin ya dace domin saita kasar don kadda a koma gidan jiya. Mahamadou Bachir Harouna Hambally sarkin karamar hukumar Djoundjou da ke yankin Dosso na daga cikin masu irin wannan tunani.

To sai dai 'yan Nijar da dama musanman masu fafutikar kare dimukuradiyya na adawa da ra'ayin wannan basarake, suma masu cewa hakan tamkar mayar da hannun agogo baya ne a game da tafarkin dimukuradiyya da aka yi nasarar dora kasar a kai bayan gwagwarmaya ta shekaru masu yawa. Alhassane Intinicar dan siyasa kuma makusancin hambararren shugaba Mohamed Bazoum, na mai tunanin cewa kadda rikon kwaryar da sojoji za ta su yi ya wuce na shekara guda kafin su tattara su fice.

Yamai lokacin gangamin goyon bayan juyin mulkiHoto: DW

Tun dai lokacin ya yi jawabinsa na farko bayan juyin mulki inda ya sanar da aniyarsa ta jan ragamar kasar na wa'adin ba zai wuce shekaru uku ba, har kawo yanzu shugaban gwamnatin mulkin sojan janar Abdourahaman Tiani bai kara sake waiwayo wannan batu ba. A halin yanzu dai 'yan Nijar sun saka ido suna jiran babban taron kasa da za a shirya nan gaba domin ka'ide lokacin da sojoji za share kan madafun iko. To amma a safukan sada zumunta mahawara na zafafa a game da zakulo wakilan da ya cancanci su halarci taron, sannan kuma ga sharadin ECOWAS na kin amincewa da mulkin rikon kwarya na sai mahadi ka ture.