Akwai telolin makwabciyar kasa Najeriya, wadanda tauraransu ke haskawa yanzu haka a fagen dinkin Hausa a birnin Yamai fadar gwamnatin Jamhuriyar Nijar. Shekaru kimanin 25 kenan da Sadisu Mustapha yake sana'ar dinki a wannan birni, ya kuma bayyana rawar da telolin Najeriya ke takawa a fagen dinki aNijar din da kuma yadda suka samu karbuwa a wajen al'umma.