1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jami'an Amirka sun sauka Turkiyya

October 17, 2019

A kokarin yayyafa wa rikicin arewacin Siriya ruwan sanyi, manyan jami'an Amirka da ke ke kokarin shiga tsakani sun isa Turkiyya domin tattauanawa da Shugaba Racep Tayyip Erdogan.

Mike Pence und Mike Pompeo
Hoto: picture-alliance/AP Photo/J. Martin

Mataimakin shugaban kasar Amirka Mike Pence da sakataren harkokin wajen kasar Mike Pompeo, sun isa Ankara babban birnin kasar Turkiyyar, domin tattaunawa kan batun neman tsagaita buda wuta a yankin arewa maso gabashin Siriya.

Manyan jami'an biyu dai za su gana ne da Shugaba Racep Tayyip Erdogan a kan batun da shugaban na Turkiyya ya yi ta yin biris a kai.

Hasali ma bayyana rashin damuwarsa Mr Erdogan din ya yi da barazanar kakaba wa kasarsa takunkuman tattalin arziki da musamman kasar Amirka ta yi.

Mike Pence, wanda ke shiga Turkiyya a karon farko a matsayinsa na mataimakin shugaban Amirka, ya sauka Turkiyyar ne 'yan sa'o'i bayan nesanta kansa da Shugaba Donald Trump daga rikicin Turkiyya da Kurdawan arewacin na Siriya.

A kalaman nasa dai, Shugaba Trump, ya ce babu ta yadda hakan ya shafi Amirka.