Kasar Amirka na zargin Cuba akan jami'anta na Diplomasiyya
June 28, 2018Talla
Ta kuma kara da cewar wannan ne karo na biyu da bincike ya tabbatar da jami'an Ddplomasiyyar Amirka da ke aiki a kasar ta Cuba wadanda ke zaune a wata unguwa da akayi tanadi don su sun kamu da wannan cuta, tun bayan billar irin ta da aka taba samu a shekara ta 2017,lamarin ya kawo adadin Amirkawan da suka kamu da cutar zuwa 26. Likitocin Amirka sun bayyana nau'in cutar da cewar ya hada da juyewar tunani,da take kare kanta gwamnatin kasar Cuba ta ce ba ta da masaniya a kan wannan batu amma za ta gudanar da bincike.