Jami'an Isra'ila sun kashe Bafalasdine
July 28, 2017Talla
Yaron dan shekaru 16 da haihuwa, Abdulrahman Abu Hameisa, ya gamu da ajalinsa ne lokacin zanga-zanga da daruruwan matasan Hamas suka fito don nuna goyon bayansu ga Falasdinawa a birnin kudus. A wannan Juma'ar ma dai sai da Isra'ilawan suka hana masu kasa da shekaru 50 da haihuwa shiga masallacin.
Daruruwan matasan falasdinu sun gudanar da bore kan hana su sallar da jami'an na Isra'ila suka yi. Rikicin Isra'ila da Falasdinawan ya kazanta cikin kwanakin nan kan matakan da Isra'ila ta dauka a masallacin birnin na Kudus.