1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jami'an Jamus da Faransa sun ziyarci Siriya

Mahmud Yaya Azare
January 3, 2025

Babbar Jami'ar diflomasiyyar Jamus Annalena Baerbock da takwaranta na Faransa sun gana da sabbin jami'an gwamnatin rikon kwarya ta 'yan tawayen Siriya. Su ne jakadun EU na farko da suka ziyarci Syria bayan kifar da Assad

Syrien I Außenministerin Baerbock und Außenminister Barrot treffen Ahmad Al-Sharaa
Hoto: Dominik Butzmann/AA/photothek/picture alliance

A wani matakin nuna goyan baya da karfafa gwiwa ga sabuwar gwamnatin rikon kwaryar Siriya bayan kifar da gwamnatin kama karya ta Bashar al Asad, kasashen Jamaus da Faransa da ke wakiltar kasashensu da kuma Tarayyar Turai a ziyararsu ta farko ga sabuwar gwamnatin masu rajin Islama sun jaddada aniyarsu ta ganin an dora kasar ta Siriya bisa sahihiyar turbar zaman lafiya da ci gaba, gami da bai wa 'yan kasar 'yancin zabinsu na rayuwa da addini ba tare da danniya ko tsangwama ba. Kamar yadda ministan harkokin wajen Jamus, Annalena Baerbock ke fadi:

Hoto: Dominik Butzmann/AA/photothek/picture alliance

"A matsayinmu na wakilan al'umomin duniya, wajibi ne mu ba wa sabuwar Siriya cikakken hadin kai don ganin ta sama wa kanta sabuwar madogarar da za ta tabbatar wa al'ummarta burinsu na samun kwanciyar hankali da cikakken zaman lafiya. A kasar da a 'yan makwanin da suka gabata, take karkashin mulkin kama karya na Bashar al Assad da yayi gwamman shekaru yana gasa wa 'yan Siriya aya a hannu, wanda muka yi ammanar cewa, hukunta shi da mukarrabansa kan aika-aikar da suka tafka, shi ne ginshikin adalci da zaman lafiya a kasar, wanda zai karfafi gwiwar wadanda aka tilasta musu yin kaura komawa kasarsu.”

Hoto: Dominik Butzmann/AA/photothek/picture alliance

Baerbock dai na yin wannan jawabi ne bayan nuna musu gidan kurkukun Sednaya da ake yi wa lakabi da "mahauta” in da aka yi amannar an halaka dubu dubatan 'yan adawan gwamnatin Assad a cikinsa.

Shi ma takwaranta na Faransa, Jean-Noël Barrot, wanda bayan ganawarsu da jagoran kasar ta Sirya, Ahmad Al-sharaa, ya yi alkawarin taimaka wa kasar wajen rubuta sabon kundin tsarin mulkin da zai biya bukatun bangarori mabanta a kasar:

"Fatar samun mutunci da y'ancin da al'ummar Siriya da dama suka sadaukar da rayukansu don samunsa ba za ta tafi a banza ba. Albarkacin goyon baya da aiki tare tsakaninmu da al'ummar Siriya, za mu tsallake wannan siradin da muke kai a yanzu don isa zuwa ga bukatumu za su tabbata a cikinta.”

 Duk da yaba wa irin kamun ludayin gwamnatin kungiyar Hayatul Tahreer Sham (HTS) din, ministocin sun ce, suna fatan jagoran sabuwar kasar ta Siriya, Ahmad Al-shaaraa, zai cika alkawuran da ya dauka na mutunta hakkokin tsirarun kabilu da mata, don karfafa wa duniya cire kungiyarsa daga jerin 'yan ta'adda dama cire wa kasar ta siriya tarin takunkumin da aka kakaba mata don sake ginata da tallafa mata, kamar yadda suka yi fatan sabuwar kasar ta Siriya ba za ta sake yarda wata kasa ta mayar da ita tungar 'yan ta'adda ba. 

Hoto: Jörg Blank/dpa/picture alliance