Jami'an Koriya da na afghanistan sun amince tattaunawa da Taliban
August 2, 2007Talla
Jamian Koriya ta kudu dana Afghanistan suna nan suna kokarin amincewa kan gurin da ya kamata su gana,bayan sun amince su gana ido da ido da yan taliban kann batun sauran yan kasar Koriya ta kudu 21 da suke garkuwa dasu.Shugaban tawagar mai shiga tsakani da Taliban yace yan kungiyar ta Taliban sun amincesu gana da jakadan Koriya ta kudu.ya zuwa yanzu dai sun kashe yan Koriyan biyu.Su dai yan kungiyar Taliban sun bukaci gwamnatin Afghanistan da ta sako abokansu data tsare a matsayin musayar wadannan yan Koriyan.Mahukuntan kasar Koriyan yanzu haka sun kama hanyar zuwa Amurkla domin neman taimakon Bush wajen kawo karshen wannan kiki kaka.