1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jami'an MDD sun jikkata a Lebanon

March 7, 2026

A kalla jami'an wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya uku ne suka jikkata a wani hari da aka kai sassaninsu da ke kudancin Lebanon.

Hoto: Rabih Daher/AFP

Dakarun UNIFIL sun ce lamarin ya faru ne bayan wani mummunan fada da aka gwabza a yankin Qawza. Ita rundunar sojin Ghana ta ce an kai hare-haren makamai masu linzami kan hedikwatarta da ke daga cikin dakarun wanzar da zaman lafiyar. A cewar sojin na Ghana, jami'anta byu sun samu mummunan rauni yayin da kuma guda ke cikin halin dimuwa.

Sai dai Majalisar Dinkin Duniya ba ta daura alhakin harin kan kowa ba. Ko da yake rundunar ta UNIFIL ta ce za ta gudanar da bincike tana mai cewa, ba za ta lamunci kai wa dakarunta da ke kan aiki hari ba.

A nashi bangaren shugaban kasar Lebanon, Joseph Aoun ya zargi Isra'ila da kaddamar da harin tare da yin tir da harin. Shi ma Shugaba Emmanuel Macron na Faransa ya yi Allah wadai da harin inda ya ce Faransa na aiki tare da wasu kasashen domin ganin an dakile yaduwar rikicin zuwa wasu sassa.