1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Jami'an sojin Lebanon da Isra'ila na ganawa a Amurka

May 29, 2026

Tattaunawar na gudana a daidai lokacin da Isra'ila ta tsananta kai hare-hare a kudancin Lebanon, tare da kaddamar da farmaki ta kasa domin fatattakar mayakan Hezbollah masu alaka da Iran.

Harin Isra'ila a kudancin Lebanon
Harin Isra'ila a kudancin LebanonHoto: Kawant Haju/AFP

Jami'an sojin Lebanon da na Isra'ila na gudanar da tattaunawa a karon farko a ranar Juma'a nan a birnin Washington na Amurka, inda Beirut za ta bukaci Tel-Aviv ta dakatar da tsananta hare-haren da take kai wa a kudancin kasar da kuma kaddamar da farmaki ta kasa.

Tawagar da ke wakiltar Lebanon a taron da ke gudana a ma'aikatar tsaro ta Pentagon, na karkashin shugaban ayyukan rundunar sojin kasar Janar Georges Rizkallah tare da rakiyar wasu mambobi guda shida. Daga bangaren Isra'ila kuwa shugaban sashen dabarun yaki na rundunar sojin kasar Janar Amichai Levin ne ke wakilitarta a taron tattaunawar da kasashen biyu suka fara tun a watan Afirilu da ya gabata.

Tsagaita wuta tsakanin Isra'ila da Lebanon ta fara aiki

Tattaunawar na gudana a daidai lokacin da Amurka da Iran ke ci gaba da kokarin cimma yarjejeniya don kawo karshen yakin Gabas ta Tsakiya inda Teheran ke son a saka Lebanon a cikin yarjejeniyar.

Sai dai Kungiyar Hezbollah na ci gaba da nuna adawa da tattaunawar, tare da kiran Lebanon da ta janye daga shiga shawarwarin, tana mai zargin Israel da kokarin tilasta yin hadin gwiwa da da Beirut domin yakarta.