1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Afganistan: Jami'an tsaro 100 sun halaka

Yusuf Bala Nayaya
August 13, 2018

A cewar ministan tsaro na Afganistan Tariq Shah Bahrami baya ga jami'an da suka rasu akwai kuma fararen hula da dama da suka rasu.

Afghanistan, Ghasni, ein afghanischer Wachmann geht während eines Taliban-Angriffs in der Stadt spazieren
Hoto: Reuters

Akalla jami'an tsaro 100 ne suka halaka a fadan da ake fafatawa da mayakan Taliban a kokarin korarsu daga birnin Ghazni na Afganistan, ministan gwamnati ya bayyana haka a wannan rana ta Litinin bayan kwanaki hudu ana fafata yaki.

A cewar ministan tsaro na Afganistan Tariq Shah Bahrami jami'an tsaro kimanin 100 sun halaka, akwai kuma fararen hula kimanin 20 zuwa 30 wadanda suma sun halaka a wannan fafatawa da aka yi da mayakan na Taliban tsawon kwanakin hudu.