1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jami'an tsaro a Dubai sun cafke Makamai da suka doshi Yemen

March 24, 2011

Rigingimun boren adawa da Gwamnati a ƙasashen Larabawa na assasa fasa ƙwaurin makamai

Hoto: DW

Jami'an 'yansa a Dubai cibiyar cinikayyar Haɗaɗɗiyar daular Larabawa , sun gano yunkurin yin fasa kwaurin makamai zuwa gunduwar Saada dake arewacin Yemen, yankin dake ƙarkashin ikon 'yan shi'a, masu adawa. Makaman da aka sauke a Dubai ta jirgin ruwa, akan hanyarsa ta zuwa arewacin na Yemen, ya kunshi Bindigogi dubu 16, waɗanda aka kera a Turkiyya. Yemen ɗin dai ta fuskanci gangamin adawa da gwamnati cikin watanni biyu da suka gabata. Masu adawar na neman hamɓarar da gwamnatin shugaba Ali Abdullah Saleh, wanda ya yi shekaru 32 akan karagar mulki. Ministan raya ƙasashe na Jamus Dirk Nieble, ya yi barazanar sanyawa shugaba Saleh takunkumi, idan har jami'an tsaro suka cigaba da amfani da karfi akan masu zanga-zangar adawa. A yanzu haka dai Jamus ta janye jami'anta 80 dake aiyukan agaji a Yemen.

Mawallafiyya: Zainab Mohammed Abubakar
Edita : Mohammad Nasir Awal