1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

'Jami'an tsaro na amfani da karfi kan 'yan adawa a Yuganda'

January 7, 2026

Jagoran adawa a kasar Robert Kyagulanyi ne ya yi wannan zargin a yayin da ake shirin gudanar da babban zabe.

Yoweri Museveni na neman wa’adi na bakwai a zaben ranar 15 ga Janairu.
Yoweri Museveni na neman wa’adi na bakwai a zaben ranar 15 ga Janairu.Hoto: Uganda PPU

Dan takarar shugaban kasar Yuganda na jam'iyyar adawa Robert Kyagulanyi  wanda aka fi sani da Bobi Wine ya zargi jami'an tsaron kasar da amfani da karfi a kansa da kuma magoya bayansa.

Bobi Wine kan sanya rigar kariya daga harsashi da hula ta soja yayin yakin neman zabe domin kare kansa daga harbin bindiga.

Museveni ya gaza hakura bayan mulkin shekaru 40

Sai dai wannan kayan kariya ba ya iya kare shi daga hayaki mai sa hawaye wanda sau da dama jami'an tsaro ke fesawa a duk inda ya ke gangamin kamfe.

Mista Wine na kalubalantar shugaba Yoweri Museveni, wanda ya ke mulkin Uganda tun a shekarar 1986, bayan ya rika sauya kundin tsarin mulkin kasar akai-akai domin ci gaba da dawwama kan mulki.

An sake kama Bobi Wine

An hana masu hamayya tsayawa takara sannan jami’an tsaro na gwamnati na halartar tarukan ‘yan adawa suna takura musu a yayin da Museveni ke neman wa’adi na bakwai a zaben ranar 15 ga Janairu.