Jami'an tsaro sun bindige wasu 'yan ta'adda a Diffa
July 12, 2015Talla
'Yan bidigar sun hallaka wani kaftin din sojan da ke tsaron gidan kason, tare da jikkata wasu sojojin biyu, amma ba tare da sun saki dan kaso ko daya ba. Jami'an tsaro da suka mayar da martani kan wannan hari sun bindige 'yan ta'addar guda uku kuma suna sanye da jigidar Bam.
Su dai 'yan bindigar da ba'a san adadinsu ba, sun kai harin ne a kafa dauke da gurneti da kuma bindigogi, kuma suna sanye da kayan sojojin na Nijar abun ma da ya basu damar kaiwa har ya gidan kason.Tuni dai jami'an tsaro ke ci gaba da zurfafa bincike, inda aka daukaka Al'kur'ani mai girma domin gano wadanda suke da hannu cikin lamarin.