1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jami'an tsaro sun kashe 'yan bindiga da dama a Katsina

March 8, 2026

Rahotanni daga jihar Katsina da ke arewa maso yammacin Najeriya sun yi nuni da cewa jami'an tsaron sun kashe 'yan bindiga kimanin 45 a karamar hukumar Danmusa da ke jihar.

Jami'an tsaro sun kashe 'yan bindiga da dama a Katsina
Hoto: James Sheehan/U.S. Army/REUTERS

Hukumomi a jihar Katsinan Najeriya sun samu nasarar kashe 'yan bindiga kimanin 45 yayin da 'yan bindigar suka kashe jami'an tsaro uku a wani artabu da aka yi tsakanin bangarorin biyu a karamar hukumar Danmusa da ke jihar. Lamarin ya faru ne lokacin da 'yan bindigar suka kai hari a garin Alhazawa, inda mutanen garin suka kashe 'yan bindiga uku. Bayan kwana guda da 'yan bindiga suka dawo daukar fansa, sai dai kuma suka gamu da fushin jami'an tsaron kamar yadda kwamishnan tsaron jihar, Dr Nasuru Ma'azu ya tabbatar

Karin bayani: Me ya sa hare-hare ke yawaita a arewacin Najeriya?

Jami'an tsaro a Najeriya na ci gaba da yunkurin murkushe 'yan bindiga yayin da har yanzu 'yan bindiga ke ci gaba da garkuwa gami da kisan al'umma.