Jami'an tsaron Kenya sun tsare wasu 'yan Birtaniya biyu a kan iyakar kasar da Somaliya
October 18, 2011A safiyar Talata, mutane garin afmadow suka ci na kare a yayin da yan kungiyar al shabaab suka fado garin suna shirin fafatawa da dakarun kassar kenya.
Wani mazauninn garin ya bayyana cewa tun jiya ne mutanen garin suka fara hijira zuwa dhobley, wani yankin dake kusa da iyakar da dakarun kenya suka ce sun kori yan tawayen daga wurin. Jiragen sama sai shawagi suke a samaniyar afmadow yayin da su kuma yan al shabaab suna ta faman haka ramuka a ciki da wajen garin.
Mamaye kasar somalia da Ehtopia ta yi daga shekarar 2006 zuwa 2008 ne ya kawo kafuwar kungiyar yan tawayen al shabaab.
Kungiyar ta karyata cewa su ne suka kame mutane 4 yan kasashen turai, a inda suka kara da cewa an dai yi amfani da kame mutanen ne kawai domin a sami dalili.
Kakakin al shabaab Sheik Ali Mohamud Rage ya ya yi kira da kasar kenya da ta janye dakarun ta daga somalia tunda babu abinda zata tsinta a somalia, idan kuma har ta yi kunnen uwar shegu da wannan kiran, to ta kuka da kanta.
Shi kuma kakakin dakarun kasar kenyan Major emmanuel chirchir ya ce al shabaab bata isa ta tsorata su ba, don haka babu abinda za'a fasa.
Yanzu haka, babu wanda zai iya cewa ga iya lokacin da dakarun kenya zasu yi a somalia, tunda an jima ana tursasa nairobi da ta dauki matakai da zasu gamsar da duniya cewa zata iya kare masu shigowa kasarta yawon bude ido ba tare da wata barazana ba.
Jakadan kasar somalia a kenya Mohammed Ali Nur ya ce kasar kenya bata da laifi.
Kasar kenya ta na yin abinda take yi ne domin ta kare kanta, kasar ta da mutanen ta.
Wani dan kasar somalia mazaunin kenya Mohammed Hussein ya ce kasar kenya ta yi daidai. Domin wanna yunkuri na kare kai ne bana tsokana ba.
"Wannan yaki na kowa da kowa ne. Bana kasar kenya ko na somalia ita kadai ba ne. Yaki ne da ake yi duk duniya gabaki daya. Don haka ya zama dole mu hada kan mu don mu yaki wadan nan mutanen."
Wakilin mu dake kasar somalia Hussein Awys shi kuwa, cewa yayi tun da yake har yanzu mutanen kasar somalia basu nuna damuwar su game da wannan al'amari ba, ita ma gwamnatin bata ce kanzil ba, to yar manuniya ta nuna cewa akwi yarjejeniya tsakaninn gwamnatocin biyu.
Kamar yarda ministan harkokin waje na kenya ya fadi cewa da iznin gwamnatin somali suka shiga, amma har yanzu ita gwamnatin somalia dai ko uffan bata ce ba. Ba mamaki haka yana da nasaba ne da hango hanyar magance kungiyar al shabaab da gwamnati somalia ta yi.
Mawallafiya: Hawwah Abdullahi Gambo
Edita: Zainab Mohammed Abubakar