1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Fitar takardun karatun Tinubu na tada kura a Najeriya

Ubale Musa Abdoulaye Mamane
October 3, 2023

Bayan dogon lokaci ana kace-nace, daga karshe jami'ar Chicago dake kasar Amurka ta fitar da takardun karatun Bola Tinubu, sai dai fadar shugaban kasar ta ce Ko Gezau.

Nigeria | Bola Tinubu |  Shugaban Kasa
Nigeria | Bola Tinubu | Shugaban Kasa Hoto: Sunday Aghaeze/Nigeria State House via AP/picture alliance

Wasu sun ce sunansa Lamidi Amoda, wasu  kuma suka ce cikin sunan mata yaje karatu a kasar Amurka, ga shugaban tarrayar Najeriya dake fafutukar kubcewa masu adawar da ke ta neman kwace goruba a hannun kuturu.

Madugun adawa a kasar Atiku Abubakar ne dai ya nemi jami'ar Chicago ta  Amurka da ta fitar da cikkakun takardun karatun shugaban na Najeriya Bola Tinubu.

Karin Bayani:  Takardun Tinubu da mataimakinsa sun yi 'batan-dabo'

Shugaba Tinubun ya share shekara da shekaru yana fuskantar zargin amfani da takardun bogi a lokacin karatunsa na jami'a, sabbabin takardun da suka hada da shaidar kamalla jami'ar, ko bayan takardu na karatu na wata kwalejin share fage ta jami'ar dai sun yi karin haske bisa shugaban, dama iliminsa.

Babban buri a bangaren masu adawar dai na zaman tabbatar da karya a takardun shugaban da kuma ke iya kai shi ga rasa kujera ta shugaban kasar Najeriya.

Karin Bayani:  Kotu za ta yanke hukunci kan zaben Najeriya na 2023

Senata Umar Tsauri na zaman jigon jam'iyyar PDP mai adawa da kuma yace "Tuni kwalliya ta iya kai wa ga wanke sabulu a fatan tabbatar da burinsu."

Kokarin komawar kallo zuwa sama, ko kuma cika buri na siyasa, dai in har 'yan lemar suna ta tsalen murna, ga masu tsintsiyar ko gezau domin hakan baya da tasiri a cikin fage na siyasar Najeriya, kana "Duk wannan maganar zancen banza ne" in ji Abdul Aziz Abdul Aziz kakakin shugaban Najeriyar Bola Ahmed Tinubu

Karin Bayani:  Kwanaki 100 na gwamnati a Najeriya

A kowane lokaci daga yanzun ana saran kotun kolin ta fara zaman nazarin shari'ar ta shugaban kasa, kana dokar zabe ta kasar dai ta tanadi tsawon wattani guda biyu na yanke hukunci bisa shari'un zaben Najeriya.