Jamiyar ANPP ta lashi takobin yaki da cin hanci a Najeriya
December 19, 2006Talla
Jamiyar ANPP a taraiyar Najeriya ta lashi takobin kakkabe miyagun halaye da cin hanci da rashawa a kasar dake yammacin Afrika.
Jamiyar ta fadi haka ne a lokacinda take sanarda wanda ta zaba a matsayin dan takarar shugaban kasar.
A dai jiya ne jamiyar ta ANPP ta tsaida tsohon shugaban mulkin soji Janar Muhammadu buhari mai ritaya,bayanda sauran yan takara 6 suka janye daf da fara jefa kuriar,suna masu fadin cewa tsohon shugaban na soji shike da kwarewa tare da dama mafi yawa na lashe zaben da zaa gudanar a 2007.