1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jam´iyun adawa a Senegal sun ƙauracewa zaɓen majalisar dattawa

August 17, 2007

Jam´iyun adawa a ƙasar Senegal, sun yanke shawara ƙauracewa zaɓen yan majalisun dattawa da za a shirya ranar lahadi mai zuwa.

Kamar yadda kudin tsarin mulkin ƙasar ya tanada, yan majalisun dokoki, tare da kansilolin ƙasar baki ɗaya ke da yaunin zaɓen majalisar dattijai.

Yan adawar Senegal, sun ɗauki matakin ƙauracewa wannan zaɓe ta la´akari da maguɗin da ke tattare da shi a cewar su.

A shekara ta 2001 ne shugaban kasa Abdulahi wade ya rusa majalisar dattawan a dalilin ƙarancin kuɗin gudanar da ayyuka.

Saidai a yayin da ya ke gudanar da yaƙin neman zaɓe a shekara da ta gabata, shugaban ƙasar Senegal, ya alkawarta sake farfaɗo da wannan Majalisa, da zaran yayi nasara sake hawa kan karagar mulkin ƙasar.