Burundi ta samu sabonn shugaban kasa
May 25, 2020Talla
Hukumar zaben kasar ta ce Evariste Ndayishimiye ya samu kaso 68.72 na kuru'un da aka kada, lamarin da ya ba shi damar lashe zaben shugaban kasar ta Burundi.
Hukumar zaben ta ce madugun adawa Agathon Rwasa da ya yi takara a jami'iyyar National Freedom Council ya samu kaso 24.19 na kuru'un da aka kada. Sai dai ba da jimawa ba madugun adawar da jam'iyyarsa sun yi watsi da sakamakon zaben, suna zargin an yi danniya da munakisa a zaben shugaban kasar. Jam'iyyar ta National Freedom Council ta yi zargin hukumomi sun kame wakilanta a rumfunan zabe don bayar da damar rubuta irin sakamakon zaben da ake so.
Zaben na Burundi dai ya gudana ba tare da masu sanya ido daga kasashen ketare ba a saboda annobar coronavirus.