CDU: ta tsayar da Armin Laschet
April 20, 2021Da safiyar wannan rana ta Talata ce jam'iyyar CDU mai mulki a Jamus ta sanar da sunan Armin Laschet da ke zama gwamnan jihar NRW a matsayin dan takararta a zabukan kasar da ke tafe a watan satumbar shekarar nan ta 2021 bayan da abokinsa karawarsa na CSU Markus Söder ya janye daga takarar. Jamus na gab da sanin wa zai maye gurbin Shugabar gwamnatin Angela Merkel. Bayan an dade ana kai ruwa rana, jam'iyyar kawance ta CDU/CSU sun aminta da tsaida Armin Laschet a matsayin dan takararsu. Tun a tsakiyar Janairun wannan shekarar ce, Armin Laschet ya zama sabon shugaban jamiyyar kawance ta CDU/CSU da ke shirin gadar shugabar gwamnatin Jamus a zaben kasar da ke tafe a watan Satumba. Yanzu dai Lacet mai shekaru 60 zai tsaya takarar ne, bayan da abokin karawarsa Markus Söder na jam'iyyar CSU ya janye.
Karin Bayani: Baerbock za ta jagoranci jam'iyyar The Greens a zaben 2021
Ana gani dai akwai aiki a gaban Laschet musamman ma idan aka yi la'akari da yadda jam'iyyar "The Greens " masu rajin kare muhalli ke kara samun tagomashi da ma burinsu na zama jam'iyya mai fada a ji ta biyu a majalisar kasar sai dai kuma tarihi ya nuna tun shigar shi majalisar, ya kulla alaka a tsakanin jam'iyyarsa ta CDU da ta The Greens din, sai dai kamar yadda ake cewa a siyasa babu babban amini kuma babu babban makiya. Hakazalika a fagen gogewa a siyasar Turai ana ganin Laschet ya fi Merkel gogewa ko da ta zama shugabar gwamnati na wancan lokacin. ko baya ga kwarewar shi a fannin shari'a da na siyasa, ya rike manya da kananan mukamai kama daga karamar hukuma ada ta jiha da tarayar har ma a majalisar Turai.
Duk da wadannan kwarewar wata kuri'ar jin ra'ayin al'umma ta nuna cewar, kaso 32 na wadanda suka zabi CDU da CSUa shekarar 2017 sun ce, za su zabi Laschet amma da dama na ganin kamar Markus Söder ya fi shi yin suna a tsakanin Jamusawa. Yanzu haka dai Armin Laschet zai yi takara da Annalena Baerbock mace daga jam'iyyar The Greens masu rajin kare muhalli da kuma Olaf Scholz ministan kudi na jam'iyyar SPD da ke cikin kawancen gwamnatin Jamus.