1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Jam'iyyar Abiy ta lashe zaben 'yan majalisa a Habasha

June 21, 2026

Jam'iyyar Prosperity Party (PP) ta samu rinjaye a zaben 'yan majalisa, inda ta samu kaso 90 cikin 100 na yawan kujeru.

Firaministan Habasha Abiy Ahmed
Firaministan Habasha Abiy Ahmed Hoto: Ethiopia News Agency/Handout/REUTERS

Abiy, wanda ke kan karagar mulki tun daga 2018, na fuskantar matsin lamba daga ciki da wajen kasar, kan yadda yake gudanar da mulkin kama karya, musamman alakarsa da makwabciyar kasar Eritrea, wanda ke zama kalubale ga lambar Nobel ta zaman lafiya da yake rike da ita.

Karin bayani:Tasirin rashin yin zabe a wasu yankuna a Habasha

Shugaban Hukumar Zaben Habasha, Melatwork Hailu, ya ce jam'iyyar (PP) ta samu kujeru 438 daga cikin 486 na majalisar wakilai, a zabukan da aka gudanar a mazabu 501 daga cikin 547 da ke fadin kasar. Jam`iyyu akalla 40 ne suka shiga zaben, to amma sun kasa kai bantensu sakamakon rashin kudin shiga da tsare-tsare.

Karin bayani:An bude rumfunan zaben 'yan majalisa a Habasha

To sai dai kamar yadda aka tsara tun da fari, ba a gudanar da zabe a yankin arewacin Tigray ba, yankin da ke farfadowa daga yakin basasar shekara ta 2020 zuwa 2022, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane sama da 600,000.