Jam'iyyar adawa ta samu rinjaye a majalisar Cape Verde
May 29, 2026
Babbar jam'iyyar adawa a Cape Verde ta lashe zaben 'yan majalisar dokokin kasar da aka gudanar a ranar 17 ga watan Mayu da kashi 48.04% na kuri'un da aka kada, lamarin da ya ba ta cikakken rinjaye a majalisar kamar yadda sakamakon da hukumar zaben kasar ta fitar ya nuna.
Jami'ayyar ta PAICV ta samu kujeru 37 cikin 72 na majalisar dokokin, kuma ana sa ran shugabanta Francisco Carvalho zai karbi mukamin firaminista nan ba da jimawa ba.
Francisco Carvalho, wanda tun bayan fitar da sakamakon wucin gadi na zaben a ranar 18 ga watan Mayu ya ayyana kansa a matsayin wanda ya yi nasara, zai maye gurbin Ulisses Correia e Silva wanda ya shafe shekaru 10 yana jagorantar gwamnatin Cape Verde.
Tsibirin Cape Verde mai al'umma kusan 520,000 na a tsakiyar Tekun Atlantika a tazarar kilomita 600 daga gabar Senegal, kuma ana kallonsa a matsayin daya daga cikin kasashen Afirka masu kyakkyawan tsarin dimokuradiyya.