1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

'Jam'iyyar AfD mai kyamar baki ce mafita'

December 29, 2024

Fitaccen attajirin nan na Amurka Elon Musk ya sake jaddada goyon baya ga jam'iyyar AfD ta Jamus mai ra'ayin kyamar baki, inda ya ce jam'iyyar ce mafita ga siyasar kasar.

Attajirin Amurka kuma shugaban kamfanin shafin X Elon Musk
Attajirin Amurka kuma shugaban kamfanin shafin X Elon Musk Hoto: Alain Jocard/AFP [M]

Musk ya bayyana hakan ne a yayin zantawarsa da jaridar Welt, kuma kalaman nasa na zuwa ne makonni bakwai gabanin babban zaben kafin wa'adi da za a gudanar a nan Tarayyar Jamus.

Karin bayani: Yan siyasar Jamus sun caccaki Musk kan AfD

Attajarin ya kuma kore shakkun masu kada kuri'a kan yadda ake alakanta jam'iyyarta AfD da batun kyamar baki, inda ya ce sam ba haka lamarin yake ba. Wasu daga cikin 'yan majalisar dokokin Jamus sun gargadi Elon Musk kan yadda yake shiga sabgar siyasar Jamus.

Karin bayani: Harin Magdeburg zai zama maudi'i a yakin neman zaben Jamus?

A shekara ta 2021, hukumar da ke tattara bayanan sirri ta Jamus ta yi zargin cewa manufofin jam'iyyar AfD na da alaka da tsattsauran ra'ayi na kyamar baki.