1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jam'iyyar AfD na samun tagomashi a zaben gabashin Jamus

September 1, 2024

Magoya bayan jam'iyyar AfD sun yi fitar kwari a zaben da ake yi a wasu jihohi biyu na gabashin kasar. Zabe ne dai da baki ke fargabar samun rinjayen jam'iyyar saboda tsananin ra'ayinta.

Hoto: Marco Steinbrenner/DeFodi Images/picture alliance

Ana kada kuri'a a zaben da ake yi a jihohin Thuringa da Saxony na nan Jamus, zaben kuma da baki 'yan kasashen wajen da ke zaune a can ke fargabar samun nasarar jam'iyyar nan ta AfD ta masu tsananin kishin kasa.

Zaben na yau dai zakaran gwajin dafi na irin karfin da jam'iyyar ta AfD ke da shi a jihohin biyu ganin yadda jam'iyyar ta kara karfi a yankunan.

Dalibai ma da ke karatu a Jamus musamman ma dai johohin da jam'iyyar AfD din ke da rinjaye na nuna fargabar abin da zai biyo baya.

An dai lura da fitowar masu kada kuri'a da dama fiye da zabukan da aka yi a baya a jihohin duka biyu.

Da karfe shida na yammacin yau agogon Jamus ne, wato hudu agogon GMT ne za a rufe rumfunan zabe.

Tsallake zuwa bangare na gaba Babban labarin DW

Babban labarin DW

Tsallake zuwa bangare na gaba Karin labarai daga DW

Karin labarai daga DW