Jam'iyyar AfD ta kayar da CDU ta Merkel
September 4, 2016
A bisa alkaluman kididdiga da gidan Talabijin na ZDF ya fitar, Jam'iyyar Afd mai kyamar baki ta sami kashi 21.5 cikin dari na kuri'un da aka kada.Hakan na nufin cewar a karon farko jam'iyyar za ta shiga majalisar dokokin jihar ta arewa maso gabashin Jamus. Da ma dai tana da wakilai a majalisun dokoki a jihohi takwas na tarayyar Jamus.Akwai kuma yiwuwar cewar jam'iyyar na iya samun damar shiga majalisar tarayya ta kasa a babban zabe da za'a yi a shekara mai zuwa.
A waje guda dai Jam'iyyar CDU ta shugabar gwamnati Angela Merkel ta sami kashi 20 ne cikin dari na kuri'un da aka kada a zaben na yau, wanda ke nufin cewar ta fado zuwa matsayi na uku a jerin jam'iyyun da ke da karfi a jihar ta Mecklenburg Vorpommern . Mutane kimanin miliyan daya da dubu dari uku ne suka kada kuri'a zaben.