1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikici ya dagule a jam'iyyar APC mai mulkin Nageriya

March 6, 2020

Adams Oshiomhole shugaban jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya ya zargi wasu mambobin jam'iyyar da hada rikicin domin cinma wani buri na siyasa.

Abuja, Partei Kongress der in Nigeria regierenden APC
Hoto: DW/U.Musa

Shugaban Jam'iyyar APC mai mulki ya ce rikicin cikin gidan da ya barke a cikin jam'iyyar na da ruwa da tsaki da gwagwarmayar mallakin ruhin jam'iyyar domin zaben shekara ta 2023.

 A wata Hirar da tashar DW Adams Oshiomhole ya ce wasu gwamnonin jam'iyyar guda uku ne ke jagorancin yunkurin tsige shi da nufin neman damar samun shugabancin kasar a shekara ta 2023.

Shugaban jam'iyyar ya ce baya aiki ga jagoran jam'iyyar Bola Ahmed Tinubu, kuma ba shi da wani tasiri wajen fitar da dan takara na shugaban kasar jam'iyyar a zaben na gaba.

Wani rikicin cikin gida tsakanin manyan 'ya'yan APC dai ya kalli wasu kotuna guda biyu yanke hukuncin da ya saba a bisa makomar shugaban da ma kila jam'iyyar da ke neman dorawa a cikin babakeren mulki na kasar

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani