1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jam'iyyar APC na fuskantar kalubale daga matasa

February 5, 2021

Wani sabon rikici ya kunno kai tsakanin matasan APC mai mulkin Najeriya da ke son a sakar musu ragamar gudanarwa da kuma tsofaffi da suka mamaye ragamar mulki, lamarin da ke zaman alamun tawaye a cikin jam'iyyar.

Nigeria Wahlkampf Mohammadu Buhari & Yemi Osinbajo
Gwamnatin Buhari na fuskantar kalubale daga matasaHoto: Chris Stein/AFP/Getty Images

A wani abun da ke zaman alamun tawaye a cikin harkokin jam'iyyar APC mai mulkin tarrayar Najeriya, matasa sun ce tura ta kai bango, kuma hakuri ya kare a cikin yadda harkoki ke tafiya a cikin harkokin mulki na kasar. Sama da kuri'a miliyan tara ne matasan tarrayar Najeriya suka kada wa jam'iyyar APC ta masu tsintsiya a babban zaben da ya kai ta bisa gadon mulki na kasar shekaru shida baya. Saii dai kasa da kaso 3% na masu mukamai a gwamnatin APC ne ke zama na matasan da ke a tsakanin shekaru 18 zuwa ga 40 a kasar. Abun da matasan ke fadin cewa da sauran sake a cikin harkokin mulki na kasar.

Jam'iyyar APc ba ta cika ba wa matasa mukamai baHoto: DW/K. Gänsler

 Matasan sun kalli idon shugaban kasar suka ce masa lokaci ya zo ga matasa na kasar da ke zaman kaso 60% na daukar mulki a kasar da tun bayan 1999 ke zaman hurumin dattawa. Matasan sun ce sun kawo karfi, kuma suna bukatar sauyi da nufin cika burin sauyin da kasar take da bukata yanzu.

Barrister Isma'ila Ahmed, shugaban matasa na riko  na kasa a  jam'iyyar APC jagoranci kokarin neman sauyin ya zuwa fadar gwamnatin kasar. Amma kuma matasan na kallon dama a cikin sabon tsarin sake rijistar da jam'iyyar ta kaddamar a makon daya shude. Sun koma baya cikin harkar mulki ne bisa zargin rashin iya taka rawa mai kyau a mukamai dabam dabam cikin kasar can baya.

 Sai dai kuma a fadar  Abubakar Sadiq da ke zaman shugaban matasan jam'iyyar reshen Arewa maso yammacin kasar, tarrayar Najeriyar na fuskantar barazanar rasa shugabanni a gaba sakamakon ware matasan daga harkar mulki yanzu.

Ana kallon sabon yunkurin da idanun bore a cikin harkokin APC da tuni ta yi nisa a cikin gwagwarmayar dorawa bisa mulkin amma ba tare da karkatar da tunani ya zuwa ga matasan ba. Tun kafin masu siyasar da ragowar matasan tarrayar Najeriyar sun hau ga tituna cikin sunan kare tana'atti na 'yan sandan SARS, amma kuma suka rikide ya zuwa wasoso na dukiya cikin kasar.

 

Matasan APC na son taka rawa a gwamnati

This browser does not support the audio element.