Goshwen ya zama sabon shugaban APC
July 24, 2025
Dan shekaru 57 kuma minista a gwamnatin kasar, Farfesa Nentawe Yilwatda Goshwe dai ya samu amincewa ta masu tsintsiyar ba tare da takarar da aka zata ba.
Sabon shugaban jam‘iyyar APC Farfesa Nentawe Yilwatda Goshwe ke nan ke rantsuwar kamun aiki yayin wani taro na jiga jigan 'ya'yan jam'iyyar a Abuja. Masu tsintsiyar dai sun zabo Goshwe ne ba tare da wata hammaya ba a wajen taron da ya samu halarta ta shugaban kasar dama gwamnonin jam'iyyar ko bayan manyan jiga jigan yayan APC.
Karin bayani: 'Yan hamayya sun razana masu mulkin Najeriya
Cikin daren jiya ne dai wani taron gwamnonin jam'iyyar da shugaban kasar ya amince kan Goshwen dan shekaru 57 kuma minister a gwamnatin ta Tinubu. Sabon shugaban dai na shirin kamun aiki a cikin jeri na kalubalen dake gaban APC da ko bayan rashi na mutum mafi farin jini cikin daurin na tsintsiya, ke kuma kallon karuwar bugun kirjin masu adawar.
Masu adawar dai na nunin yatsa ga masu tsintsiyar tare da fassarar rashin Buhari da karshen kuri'un gadon APC miliyan 12. Sanata Ahmed Lawal dai na zaman tsóhon shugaban majalisar dattawa ta kasar, kuma daya a cikin jiga jigan jam'iyyar APC da kuma ya ce masu tsintsiyar suna bukatar gyara zama kan hanya na zawarcin kuri'un gadon marigayin.
Karin bayani: ADC: Sabuwar alkiblar adawa a Najeriya
Ko bayan lallashin 'yan zaben gadon dai Goswen na kallon tururuwa cikin APC da ta kai ta ga gwamnoni 23, sannan kuma da kusan biyu a cikin ikon a mallakin majalisun kasra guda biyu. Farin jinni mai girma amma kuma kafar rigingimu na buri a cikin jam'iyyar. Ko ta ina sabo na shugaban da masu mara masa baya ke shirin su bi wajen tabbatar da ingancin daurin na masu tsintsiya, daga dukka na alamu jam'iyyar ta dau lallashi da nufin kwantar da hankula bisa jerin sauyin.
Karin bayani: Atiku ya raba gari da PDP
Shugaba Tinubu dai alal ga misali ya sanar da nada tsohon shugaban Umar Ganduje domin jagorantar wata sabuwa ta cibiyar dabarun mulkin jam'iyyar da gwamnatin kasar ta sanar a wannan Alhamis. Abun kuma da ya dadada ran 'ya'yan APC na kanon da ke fadin nadin Gandujen ya tabbatar da sake karrama su cikin jam'iyyar.
'Yan kwanaki da kila ma watannin da ke tafe dai ne ke shirin zaman zakaran gwajin dafi ga sabon shugabancin APC da ke da jan aikin iya tunkarar guguwa ta neman sauyin da ke kadawa cikin kasar a halin yanzu.