1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jam'iyyar APC ta zabi shugabannin wucin gadi

Usman ShehuJune 26, 2013

A Najeriya jam'iyyar APC ta fara cika sharuddan samun rajista kamar yadda INEC ta umarta

Gen. Muhammadu Buhari, presidential candidate of the Congress for Progressive Change, attends a campaign rally in Lagos, Nigeria, Wednesday, April 6, 2011. Buhari, a former military ruler of Nigeria, has gained support in his third bid to become president of the oil-rich nation. Buhari ruled Nigeria from 1983 to 1985 after a military coup deposed the elected president. (AP Photo/Sunday Alamba)
General Muhammadu BuhariHoto: AP

Sun dai hada da sabbabin jini dama tsoffafin da jinin nasu ke shirin tsinkewa. Sun kuma kunshi tsoffafi na 'ya'yan PDP da kuma wanda ba su taba haduwa ko da hanyar shiga kasuwa ba. To sai dai sun kai ga nasarar  hadewa ya zuwa sabuwar jamiyyar APC da ta yi nasarar basu damar jagorar harkokin ta zuwa wani lokaci.

Karkashin jagorancin Chief Bisi Akande da ya dauki gwagwarmayar shugabantar A C N dai, sabbabin shugabannin sun hada da Tijjani Musa Tumsah da aka zaba domin zama sakataren na APC. Sauran sabbabin shugabnnin sun hada da Aminu Bello Masari da ke zaman tsohon shugaban majalisar wakilan kasar, yanzu haka kuma sabon mataimakin shugaban jam'iyar na kasa. Sai Mallam Nasiru Ahmadu El-Rufai dake zaman tsohon ministan babban birnin Tarayyar Najeriyar na Abuja, da yanzu haka kuma aka baiwa mukamin mataimakin sakataren APC.

Ibrahim Shekarau ANPP da Nuhu Ribadu ACNHoto: AP

Ana dai kallon sabon shugabancin a matsayin tsallake siradin farko ga APC da ta dauki tsawon lokaci tana kokarin cika ka'idojin samun rijista domin taka rawa a cikin harkokin siyasar kasar. Rawar kuma da ya zuwa yanzu ta banbanta a zukatan su kansu 'yan siyasar kasar kama daga na PDP mai shirin ji a jikin tasirin APC da kuma tsohon ma'ajinta na kasa Bala Bawa Kaoje, yace lale marhabin da abun da suke shirin gani a siyasar.

Helkwatar jam'iyyar ACNHoto: DW/U. Musa

Hammayar gyara ko kuma hammayar kwace mulki, ana dai kallon bullar shugabancin a matsayin kama hanyar komawa bisa tsohon tsarin siyasar dake da jamiyyu biyu masu karfi, tsarin kuma da ya mamaye fagen siyasar kasar a cikin sama da shekaru 50 na yancin kanta. To sai dai kuma in har tunanin Balan PDP kwace goruba a hannun kuturu sai an shirya, ga Bala Jibrin dake zaman sabon mataimakin mai binciken kudin APC, yace su basu da shirin taimakawa PDP gyara kura-kuranta ba.

Taimakawa al'ummar Najeriya ko kuma wayon aci dai, bullar sabon shugabancin na zaman alamu na irin sabuwar alkiblar da siyasar kasar take shirin fuskanta. Alkinblar kuma da a karon farko ke iya sauyawa daga gabashin PDP da 'yan kasar suka share shekaru kusan 15 suna kallo domin neman mafita da ci gabansu.

Shugaba Goodluck Jonathan, a lokacin zaben da ya gabataHoto: AP

To sai dai kuma a tunanin Garba Umar Kari dake sharhi kan lamura na siyasar Tarayyar Najeriya, har yanzu da sauran aiki a gaban mai gonar dake shirin kisan biri don hana barnar kaka. Abun jira a gani na zaman tsallake siradin dake kama hanyar nuna alamun samar da dan takarar jamiyyar daga sashen arewacin Tarayyar Najeriyar.

Mawallafi: Ubale Musa

Edita: Usman Shehu Usman