Jam'iyyar CDU ta shugabar gwamnatin Jamus ta sake samun koma baya
May 7, 2012Masu jefa ƙuri'a a ƙasar Jamus sun zaɓi 'yan majalisar dokoki a yankin Schleswig-Holstein, inda suka kawar da jam'iyyun dake ƙawance wajen jagorancin yankin, wato Christian Democrats da kuma Liberal Free Democrats. Daya ke babu wata jam'iyyar da ta sami rinjaye kai tsaye, har yanzu ba'a san jam'iyyun da za su ƙulla ƙawancen jagorancin sabuwar gwamnatin jihar ba. Sakamakon da hukumomi suka fitar dai na nuni da cewar CDU ta shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta sami kashi 30.9 cikin 100, wanda shi ne mafi muni tun a shekara ta 1950. Sai kuma jam'iyyar Social Democrats, wadda ta sami kashi 29.9 cikin 100, wadda kuma ta ce za ta ƙafa gwamnatin ƙawance tare da jam'iyyar The Greens dake fafutukar kare muhalli da kuma ta 'yan Danish marasa rinjaye.
A baya bayannan dai jam'iyyar shugabar gwamnati Angela Merkel ta rasa jagorancin ta ne a wasu jihohin ƙasar guda ukku cikin tsukin shekaru biyun da suka gabata. Manyan jam'iyyun da suka yi gagarumar nasara a zaɓukan na wannan Lahadin dai su ne na Pirates da kaso 8.5 cikin 100 da kuma Liberal Free Democrats da kashi 8 cikin 100 na sakamakon zaɓen.
Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : mouhamadou Awal Balarabe