1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jam'iyyar Democrats ta Amirka ta yi tsokaci a kan Rasha

Zulaiha Abubakar
April 27, 2018

Shugabar marasa jinjaye a majalisar dokokin kasar Amirka Nancy Pelosi ta bayyana cewar jam'iyyar Democrats na ci gaba da bincike game da zargin da aka yi wa Rasha da hannu yayin zaben shugaban kasar Donald Trump.

 Nancy Pelosi
Nancy Pelosi Hoto: picture-alliance/CNP/AdMedia/A. Edelman

Ta kuma kara da cewar duk da rahoton da kwamitin bincike na majalisar ya fitar akan batun tana kara yin kira da kakkausar murya ga 'yan jam'yyar Republican da ke zauren majalisar da su fito da bayannan bayan binciken da kwamitin ya gudanar akan zargin kasar Rasha na shiga a dama da ita cikin zaben shugaban kasar Donald Trump.