1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Japan: Jam'iyyar LDP na kan gaba a zaben majalisar dokoki

February 8, 2026

Sakamakon farko-farko da suke fitowa daga Japan sun yi nuni da cewa firanministar kasar, Sanae Takaichi, na kan gaba a zaben 'yan majalisar dokoki.

 Firanministar Japan, Sanae Takaichi
Firanministar Japan, Sanae TakaichiHoto: Kim Kyung-Hoon/REUTERS


Sakamakon farko na zaben 'yan majalisar dokokin Japan na nuna cewa jam'iyyar Firanminista Sanae Takaichi ta LDP za ta lashe kujeru mafi yawa cikin 465 na majalisar kasar, hasalima jam'iyyar da kawayenta na iya lashe kaso 2 bisa 3 na kujerun kamar yadda kafar watsa labaran kasar ta NHK ta rawaito.

Karin bayani: An bude runfunan zaben 'yan majalisar dokoki a Japan

Jam'iyyar LDP ta mulki Japan a lokuta mafi yawa cikin shekaru 70, sai dai kuma ta rasa rinjaye a majalisar kasar sakamakon dambarwar siyasa da ta kunno kai.