SiyasaJamus
Jam'iyyar hamayya na gaba a zaben Zambiya
August 14, 2021Talla
Sakamakon na nunin cewa babban dan hamayya a Zambiya, Hakainde Hichilema, na gaba da abin da shugaba mai ci Edgar Lungu ya samu, kamar yadda hukumar zabe ta nunar a yau.
Mr. Hichilema na da kuri'u dubu 171 da 604 yayin da Shugaba Lungun ke da dubu 110 da 178 cikin manyan mazabu 15 da shugaban ke da karfi a cikin su.
Jimillar kuri'u dubu 296 da 210 ne dai aka kada a wadannan mazabu, a cewar wani jami'in zaben da ya zanta da kamfanin dillancin labaru na Reuters.
Ana dai ganin samun sakamakon zaben na Zambiya na iya kaiwa yammacin ranar Lahadi, zaben kuma da jam'iyya mai mulki ke kurarin tana kan hanyar lashe shi.