1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Zaben majalisar dokokin Faransa

Mouhamadou Awal Balarabe RGB
June 13, 2022

Kawancen jam'iyyun da ke mara wa Shugaba Emmanuel Macron baya na tafiya kafada da kafada da masu tsattsauran ra'ayin gurguzu a zaben 'yan majalisun Faransa.

Frankreich | Wahlen 2022 | Parlament
Hoto: Bob Edme/AP Photo/picture alliance

Jam'iyyar Shugaba Emmanuel Macron na Faransa na fuskantar barazanar rasa cikakken rinjaye a majalisar dokokin kasar, a sakamakon rawar gani da manyar jam'iyyun adawa biyu suka taka a zaben 'yan majalisa da ya gudana a ranar Lahadin da ta gabata. Ko da yake an samu karancin masu kada kuri'a, amma ba za a san maci tuwo da makomar manufofin Macron ba sai bayan gudanar da zagaye na biyu na zaben a ranar Lahadi mai zuwa. 

kawancen jam'iyyun da ke mara wa shugaban Faransa baya na tafiya kafada da kafada da masu tsattsauran ra'ayin gurguzu, inda alkaluma suka nuna cewar Ensemble ta Emmanuel Macron ta samu kashi 25.75% na kuri'un da aka kada yayin da kawancen jam'iyyar Nupes na Jean-Luc Mélenchon ya tashi da kashi 25.66%.

Jam'iyyar Macron na fuskantar barazanar rasa rinjaye a majalisaHoto: Ludovic Marin/AP/Pool/picture alliance

Da alama jam'iyyar Shugaba Emmanuel Macron za ta ci gaba da kasancewa mafi karfi a zauren majalisar dokokin Faransa, amma za ta iya rasa cikakken rinjaye da take da shi, bayan da kididdigar jin ra'ayin jama'a ta nuna cewar za ta iya tattara kujeru 275, alhali ana bukatar kujeru 289 wajen samun cikakken rinjaye. Saboda haka ne Firayiministar Faransa Elisabeth Borne ke ci gaba da zawarcin 'yan kasar domin samun cikakken rinjaye.

Jean-Luc Melenchon na jam'iyya masu tsattsauran ra'ayiHoto: Daniel Cole/AP Photo/picture alliance

Cibiyoyin da ke gudanar da kididdigar jin ra'ayin jama'a sun bayyana cewar kawance Nupes da Jean Luc Melenchon ke jagoranta na iya samun kujeru 150 zuwa 210 bayan zagaye na biyu na zaben. Sai dai sakamakon zai dakushe fatansa na samun rinjaye a majalisa domin haye kujerar firmainistan kasar tare da aiwatar da manufofin da ya sa a gaba a maimakon na shugaban kasa. Ita kuwa Jam'iyyar Rassemblement National mai kyamar baki ta Marine Le Pen ta zo matsayi na uku da kusan kashi 19% na kuri'un da aka kada, lamarin da ya zarta hasashen da aka yi tun da farko, kuma zai iya ba ta damar samun wakilai 15 da ake bukata wajen kafa kungiyar ‘yan majalisun adawa a karon farko cikin tarihin jam'iyyar. Le Pen ta ce akwai bukatar kawo sauyi a tsarin zaben Faransa.

Zaben 'yan majalisu zagaye na farkoHoto: THIBAUD MORITZ/AFP

Wannan zaben ‘yan majalisun dokoki ya kama hanyar sauya fasalin yanayin siyasar Faransa, saboda zai iya dagula lissafin Shugaba Macron dangane da sauye-sauyen da yake niyan aiwatarwa, musamman na tsarin fansho. Sannan baya ga zama gargadi ga Shugaba Macron, ya samar da gagarumin ci gaban ga jam'iyyun da ke da tsattsauran ra'ayi, inda Jean-Luc Melenchon ke neman zame wa Macron kadangaren bakin tulu.

Daga cikin wadanda suka yi batan bakatan-tan a zaben har da dan takarar shugaban kasa mai tsattsauran ra'ayi Eric Zemmour, wanda ya tsaya takara a kudancin Faransa kuma ya sha kaye tun a zagayen farko. Yayin da a daya hannu Jean-Luc Mélenchon, wanda tsohon jemage ne a fagen siyasar Faransa ya yi nasarar zama madugun adawa, ta hanyar jagorancin kawancen da ba a taba ganin irinsa ba a tsakanin masu ra'ayin gurguzu.