1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaFaransa

Jam'iyyar Macron ta sha kaye a zaben 'yan majalisa

Ahmed Salisu
June 30, 2024

Sakamakon farko na zaben 'yan malisar dokokin Franasa ya nuna cewar jam'iyyar National Rally ta Marine Le Pen ta samu kashi 34 cikin 100 yayin da jam'iyyar Shugaba Emmanuel Macron ta samu kashi 20.5 cikin 100.

Frankreich | Emmanuel Macron | Amtseinführung 2022
Hoto: Lewis Joly/AP Photo/picture alliance

Sakamakon farko na zaben 'yan malisar dokokin Franasa ya nuna cewar jam'iyyar National Rally ta Marine Le Pen mai manufofin kyamar baki na kan gaba a kuri'un da aka kada inda ta samu kashi 34 cikin 100 yayin da jam'iyyar Shugaba Emmanuel Macron ta rabauta da kashi 20.5 cikin 100 na kuri'un.

Jim kadan bayan bayyana sakamakon farkon na zaben, Shugaban Macron ya yi kira ga 'yan kasar da su yi dukannin mai yiwuwa wajen ganin ba su bada dama ga masu ra'ayin kyamar baki su kafa gwamnati ba a zagaye na biyu na zaben wanda zai gudana a ranar Lahadin makon gobe.

Ita kuwa Marien Le Pen da ke kan gaba a zaben na yau, kira ta yi ga 'yan kasar da su bayar da gudunmawarsu wajen ganin sun kafa gwamnatin da za ta samar wa Faransawa sauyi.

Zaben 'yan majalisar mai kujeru 577 na wannan karon dai shi ne mafi girma da kasar ta gani ta fuskar yawan wadanda suka suka fita kada kuri'a.