1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jam'iyyar AFD a Jamus ta sake zaben Alice Weidel

Binta Aliyu Zurmi
July 4, 2026

Jam'iyyar AFD mai kyamar baki a Jamus ta zabi Alice Weidel domin ci gaba da jan ragamar Jam'iyyar.

Deutschland Erfurt 2026 | AfD-Parteitag | Alice Weidel hält Rede
Hoto: Karina Hessland/REUTERS

Da gagarumin rinjaye aka sake zabar shugabar wacce ta samu nasara da sama da kaso 81 cikin 100 na kuri'un da wakilan jam'iyyar suka kada.

Jam'iyyar AFD dai na ci gaba da samun tagomashi a fagen siyasar Jamus, a zaben shekarar 2025 ita ce ta zo ta biyu, inda ta samu kusan kaso 19 a babban zaben da aka kada.

Zaben da ya gudana ba tare da hamayya ba a zauren babban taron na birnin Erfut da ke gabashin Jamus, ya fuskanci fuskin masu zanga-zanga, lamarin da ya kara fiddo da rarrabuwar kawuna da jam'iyyar AFD ta haifar a daukacin kasa.

Kamfanin dillancin labarai na Jamus DPA ya ruwaito cewa 'yan sanda sun ce kimanin mutane 31,000 ne suka halarci zanga-zangar lumana, inda masu boren ke dauke da alamu rubutu da ke cewar a dakatar da jam'iyyar AFD da 'yan Nazi a daukacin kasar.

Karin Bayani :Jamus ta ayyana jam'iyyar AfD a matsayin barazana