Jam'iyyar MNSD ta soki gwamnatin Nijar
October 15, 2014 Madugun 'yan adawar kasar ta Nijar ya bayyana wanann matsayi nasa ne lokacin wani taron manema labarai da ya kira a wannan Larabar a Yamai, inda ya bayyana wa 'yan kasa sakamakon wata ganawa da ya yi da shugaban kasar a fadarsa daga ciki har da batun cire wa shugaban jam'iyyar CDS Rahama Alhaji Mahaman Usmane rigar kariya da gwamnatin ta yi.
Kimanin mintoci 30 ne madugun 'yan adawar kasar ta Nijar ya kwashe yana fedewa shugaban kasar da gwamnatinsa biri har wutsiya akan jerin wasu laifuka da yake zarginsu da aikatawa da ya ce ya bayyanawa shugaban kasar lokacin ganawar tasu wacce shi ne ya bukaci a yi ta.
Da farko dai madugun 'yan adawar ya nuna rashin jin dadinsa akan yanda ya ce shugaban kasar ta Nijar yaki aika goran gayyata ga illahirin 'yan adawa a lokacin taron jana'izar sojojin Nijar 9 da suka mutu a Mali. Abun da madugun 'yan adawar ya ce sam bai dace ba domin kuwa su sojojin kasa ne, ba wai na wani bangaren siyasa ba. Ba tare da la'akarin cewar 'yan adawa sun baiwa gwamnatin hadin kai a cikin matakin tura sojoji zuwa Mali ba.
Da yake tsokaci akan batun rigingimun siyasar da ake fuskanta
a kasar Seini Oumarou ya ce, ya nuna wa shugaban kasar fushinsa
akan abunda ya kira bita da kullin da shi da gwamnatinsa ke yiwa
'yan adawa dama neman karya jam'iyyunsu da yin barazana ga
shugabanninsu.