1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Jam'iyyar MPS ta ayyana Deby a matsayin 'dan takararta

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
January 13, 2024

Mahamat Idriss Deby mai shekaru 37, ya dare kan karagar mulkin kasar a cikin shekarar 2021, bayan da 'yan tawaye suka hallaka mahaifinsa marigayi Idriss Deby Itno, wanda ya shafe sama da shekaru 30 yana mulkin kasar

Hoto: DENIS SASSOU GUEIPEUR/AFP/Getty Images

Jam'iyyar MPS ta ayyana shugaban mulkin sojin Chadi Janar Mahamat Idriss Deby Itno a matsayin wanda zai yi mata takarar shugaban kasa a babban zaben da za a gudanar a karshen shekarar nan da muke ciki, bayan amincewar mambobin jam'iyyar.

karin bayani:Jagoran adawa a Chadi ya zama firamnista

Mahamat Idriss Deby mai shekaru 37, ya dare kan karagar mulkin kasar a cikin shekarar 2021, bayan da 'yan tawaye suka hallaka mahaifinsa marigayi Idriss Deby Itno, wanda ya shafe sama da shekaru 30 yana mulkin kasar.

karin bayani:Hukumar zaben Chadi ta ce sabon kundin tsarin mulkin kasar ya samu amincewar kashi 86 cikin 100 na al'umma

A cikin watan Disamban shekarar da ta gabata ne dai aka gudanar da zaben raba gardama da ya fayyace irin kundin tsarin mulkin da kasar za ta yi amfani da shi, inda kuma aka nada jagoran 'yan adawar kasar Succes Masra a matsayin firmainistan kasar ta Chadi.