1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jam'iyyar Biya ta je yakin neman zabe yankin Ingilishi

Ramatu Garba Baba M K
October 4, 2018

A Kamaru jam'iyya mai mulki ta Shugaba Paul Biya ta gudanar da yakin neman zabenta a yankin da ke anfani da Turancin Ingilishi duk kuwa da barazanar da ake fuskanta daga bangaren 'yan neman aware.

Wahl in Kamerun Paul Biya
Hoto: AP

Hukumomi dai  sun ce an yi awon gaba da 'ya'yan jam'iyyar mai mulki akalla takwas tare da kai wa wasunsu hari, sai dai duk da hakan, hukumar zaben kasar ELECAM ta bayar da tabbacin gudanar da sahihin zabe.

Gabannin zaben na ranar bakwai ga wannan watan ne aka wayi gari da jin karar harbe-harben bindiga a musayar wuta a tsakanin dakarun gwamnati da bangaren 'yan aware masu gwagwarmaya da makamai, an yi ta jin karar ne a yankin Buya na masu anfani da Turancin Ingilishin a yayin da tawagar magoya bayan Shugaba Paul Biya suka zo wucewa zuwa don ci gaba da yakin neman zabe a Mamfe, magoya bayan Biya da dama ne suka sami rauni.

Elung Paul Che, shi ya jagoranci ayarin ya ce sun dauki wannan mataki duk da hadarin da ke tattare da shi saboda kaunar da suke yi wa Biya da kuma kasar ta Kamaru.

"Tun lokacin da wannan kasa ke cikin wani yanayi na hargitsi bayan kafa jam'iyyar hadaka, Kupe Maanenguba ya tsaya wa jam'iyyar ta CPDM. Saboda haka ba gudu ba ja da baya mun kudiri aniyar tsayawa da jam'iyyar abin da zan fada muku shi ya kawo mu nan''

Ana dai cikin dari-dari a yankin da ke Ingilishi a KamaruHoto: Getty Images/AFP

Kadan dai daga cikin magoya bayansu ne suka iya fitowa da dama sun tsere amma Rudulf Arrey mai shekaru 24 ya ce ya zabi fitowa don ya ji Biya shi kadai zai iya warware matsalar da ake ciki.

"Yan awaren sun hasala ka ga har sun tsayar da ranar ashirin da biyar na hana zirga-zirga, abin da ke nufin duk wanda aka samu yana yawo za a iya kashe shi ko a yi garkuwa da shi, hakazalika jami'an tsaron da aka jibge sun kasance babban barazana, ka ga suna razana jama'a saboda haka bamu da tabbacin abin da zai iya faruwa.''

Tun a ranar Talatar da ta gabata ake dakon zuwa Shugaba Biya a yankin na Buya, sai dai bai je ba babu kuma bayanin kin zuwan, amma Gerald Ngalla, daya daga cikin 'ya'yan jam'iyyar, Biya na fargabar zuwansa ka iya haifar da zubar da jini tun da 'yan awaren sun ce ba yadda za a gudanar da zabe a yankinsu. Kingsley ya zargi 'yan takara na jam'iyyar adawa da rura wutar rikicin tun da basu taba kai ziyara yankin ba.

Jam'iyyun adawa sun kaurace wa yankin da ke fama da rikicin. A makon da ya gabata dan takara Akere Muna na jam'iyyar FDP ya kai ziyarar garin Mutengene na masu anfani da Turancin Ingilishi amma rikici ya barke inda mutane hudu suka rasa rayukansu.

Masu kada kuri'a miliyan shida da dubu dari shida ne ake tsammani za su fita tashoshin kada kuri'a 2500 a yankunan na Kamaru inda za a yi zabe a ranar bakwai ga watan nan na Oktoba don zaben shugaban kasa yayin da a bangaren adawa ake ci gaba da samun rabuwar kai.

 

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani